Quran Touch

سُورَةُ التكاثر

Sura At-Takaathur

Sura 102 · 8 ayoyi · Makkiyya · Izu 30 · Mushaf Shafi 600

Saurari surar gaba ɗaya Karatu: Mishary Rashid Alafasy
Aa
  1. 102:1

    بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ أَلْهَىٰكُمُ ٱلتَّكَاثُرُ

    Alhakumu alttakathuru

    Alfahari da yawan dũkiya da dangi ya shagaltar da ku (dagaibada mai amfaninku).

  2. 102:2

    حَتَّىٰ زُرْتُمُ ٱلْمَقَابِرَ

    Hatta zurtumu almaqabira

    Har kuka ziyarci kaburbura.

  3. 102:3

    كَلَّا سَوْفَ تَعْلَمُونَ

    Kalla sawfa taAAlamoona

    A'aha! (Nan gaba) zã ku sani.

  4. 102:4

    ثُمَّ كَلَّا سَوْفَ تَعْلَمُونَ

    Thumma kalla sawfa taAAlamoona

    Sa'an nan, tabbas, zã ku sani.

  5. 102:5

    كَلَّا لَوْ تَعْلَمُونَ عِلْمَ ٱلْيَقِينِ

    Kalla law taAAlamoona AAilma alyaqeeni

    Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni.

  6. 102:6

    لَتَرَوُنَّ ٱلْجَحِيمَ

    Latarawunna aljaheema

    Lalle ne da kuna ganin Jahĩm.

  7. 102:7

    ثُمَّ لَتَرَوُنَّهَا عَيْنَ ٱلْيَقِينِ

    Thumma latarawunnaha AAayna alyaqeeni

    Sa'an nan lalle ne za ku gan ta, da idanu, bayyane.

  8. 102:8

    ثُمَّ لَتُسْـَٔلُنَّ يَوْمَئِذٍ عَنِ ٱلنَّعِيمِ

    Thumma latusalunna yawmaithin AAani alnnaAAeemi

    Sa'an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar (da aka yi muku).

Fassarar Hausa: Abubakar Mahmoud Gumi (Gumi) — Rubutun Alƙur'ani da fassara: Tanzil.net · Audio: EveryAyah.com, QuranicAudio.com

Karanta a wasu harsuna

EnglishالعربيةবাংলাاردوBahasa IndonesiaTürkçeFrançaisBahasa MelayuفارسیNederlands